Gwamnatin Saudiyya zata kashe dala biliyan 35 ba ga mahajjata ba, a'a, ga masu shaqatawa
- Kasashen musulmi na ganin Saudiyya a matsayin limamiya a harkar addinin Islama
- Saudiyyar ta kawo sauye-sauye da suke daure wa musulmin kayi, inda suke ganin kamar dujal ne ya iso
- Ta'addanci da kungiyoyi keyi da sunan addinin Islama ya sanya shugabannin sauya akalar kasar su
A jiya ne, masarautar Saudiyya ta bayyana wani sabon shiri da za'a kashe dala biiyan akalla 35, kusan Titiliyan goma na nairori, wadda za'a kashe kan harkar fina-finai da shakatawar samarii da turawa masu ziyarar kasar kafin 2020.
Kudaden za'a samar dasu ne domin a saukaka zafin ra'ayin addinin Islama a kasar ta Saudiyya, wannan kua na nufin wasu kasashen musulmin zasu koma kallon kasar ta Saudiyya a matsayin kasar badala ba ta qara imani ba.
DUBA WANNAN: Ashe N100 aka barnatar kan takurawa Dino Melaye
A lokacin da ake kaddamar da shirin, an ga wasu manyan 'yan fim na Turawa da bakaken fata, kamar su Idris Elba da Katie Holmes a taron.
Yariman Saudiyyar dai yace akalla nan da 2030, kasar ta Saudiyya zata sanya kanta a cikin kasashe masu karbar bakin duniya don watayawa.
Ga alama dai aikin hajji na iya zama wani abin koma baya a idon 'yan kasar ta Saudiyya da ma Musulmi yayin ziyartar kasar mai tsarki, domin badala da tsiraici na iya karuwa a kasar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng