Aikin banza: Ashe miliyan 100 INEC ta kashe kan zaben kiranyen Dino Melaye

Aikin banza: Ashe miliyan 100 INEC ta kashe kan zaben kiranyen Dino Melaye

- Bayan miliyoyin jama'a da suke neman jari ko da na 10,000 ne, akan sanata daya aka kashe miliyan 100

- Rikicin dai gwamnan da Sanatan suka sanya ya yi kamari, kuma gwamnan bayyi nasara ba

- Abin haushin shine, a bisa doka aka kashe kudin, wanda ya nuna akwai matsala da dimokuradiyyarmu

Aikin banza: Ashe miliyan 100 INEC ta kashe kan zaben kiranyen Dino Melaye
Aikin banza: Ashe miliyan 100 INEC ta kashe kan zaben kiranyen Dino Melaye

Hukumar zabe ta INEC, a yau juma'a, ta karyata batun cewa wai ta kashe Naira biliyan 100 kan zaben kiranyen Dino Melaye, wanda ya kayar da gwamnan shi a makon nan, sakamakon rigima da suke ta siyasa da bai kara wa talakawan jihar komai ba.

Farfesa Yakubu, a yayin zantawa da manema labarai, ya ce N100m kadai ce hukumar ta kashe kan zabukan, wadanda suka hada da kananan hukumomi bakwai da mazabu 551.

DUBA WANNAN: Anyi min wahayi Buhari ba zai zarce ba

A cewarr hukumar, dimokura diyya ce ta bada damar, kuma zaben ana yinsa ne kamar zaben sanata din ne, don haka yaci kudi.

Sai dai masu hangen nesa na ganin a lokacin da jama'a ke talauci da neman jari, hukumar kawai tayi barnar kudi ne a rigimar wasu 'yan siyasa biyu a jiharsu, abin haushi malam!

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel