Kungiyar musulmi ta JNI ta bukaci jama'a su farga saboda jami'an tsaro sunyi sanyi
- Kungiyar Jama'atu Nasrul Islam JNI tayi wani kira ga yan Najeriya a ranar Alhamis
- Kungiyar ta bukaci al'umma su farga kuma su sanya ido batun tsaro saboda yadda hare-hare da kara tsananta
- Kungiyar tayi ikirarin cewa hukumomin tsaro sunyi sakwa-sakwa ne shiyasa yan ta'adan suka sake yunkuro wa
A jiya Alhamis ne kungiyar addinin musulunci na Jama'atu Nasrul Islam JNI tayi kira ka yan Nageriya dasu farga saboda su kare kansu daga makiyansu da ke hare-hare a kan 'yan Nageriya.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin Khalid Abubakar, Sakatare Janar na JNI a wani taro daya gudana a Kaduna akan bam din daya tashi a Mubi wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 85 da jikkata wasu da dama.
Kungiyar ta ce ya kamata a kawo karshen kashe-kashen da akeyi a jihohin Borno, Kaduna, Nassarawa, Benue da Zamfara.
DUBA WANNAN: EFCC ta gano waso kadarori mallakar wata shugaban banki da ta boye a Dubai
"Bisa ga dukkan alamu hukumomin tsaro sunyi sakankance da cewa hare-haren sunyi sauki wanda hakan ya bawa yan ta'addan damar sake daura damarar kai sabbin hare-hare," inji sanarwan.
"Ya kamata gwamnati ta kara maida hankali akan wannan lamari, sannan ta bada wani tabbataccen hukunci ga masu aikata laifin ko hakan zai kawo karshe.
"Muna kira ga mutane su dage da addu'a da kuma neman gafarar Ubangiji akan wannan lamari.
"Ba zamu daina aikata ayyukan alkhairi ba musamman yanzu da watan Ramadana ya kusanto," inji sanarwan.
JNI ta kara da cewa ba wani mataki da ake dauka a kan irin haka face yadawa a kafafen watsa labarai musamman idan aka kaiwa musulmai hari a masallaci.
Muna kara jajantawa mutanen jihohin Kaduna, Zamfara, Nasarawa, Benue da Kebbi a kan rashe rashe da akayi a dalilin hare-haren da aka kai musu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng