Kudi a kashe ta hanya mai kyau: Ronaldo ya baiwa budurwarsa kyautar Zoben naira miliyan 300 (Hoto)
Zakaran dan kwallon Duniya, Cristiano Ronaldo ya shirya shigewa daga ciki, inda a kokarinsa na angancewa da Budurwarsa ya bata kyautar Zobe na da darajarsa ta kai naira miliyan dari uku, N300m, a matsayin kudin ‘Na gani ina so’.
Jaridar Sun UK ta ruwaito budurwar Ronaldo mai suna Georgina Rodriguez, wanda tsohuwar mai zaman shago ce ta bayyana bidiyon zoben samfurin Cartier a shafinta na kafar sadarwar zamani na Instagram.
KU KARANTA: Dalilin dake baiwa Babban sufetan Yansandan Najeriya kwarin gwiwar wulakanta majaisa ya bayyana ƙarara
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a cikin bidiyon da Georgina ta daura shafin nata na Instagram, an hangi Zoben yana kyalli, tare da farashinsa manne a jikin akwatin Zoben, sa’annan ta bi hoton da alamun zuciya dake alanta Soyayya.
Duk da cewa har yanzu Ronaldo bai auri Georgina ba, kuma bai bayyana wani shiri game auren ba, amma suna da ya mace mai suna Alana Martina tare da Georgina.
Duk a cikin bidiyon ana iya hangen Georgina zaune cikin wata katafariyar motar Alfarma mallakin Cristian Ronaldo, kamar yadda majiyarmu ta tabbatar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng