Kaico! Injin surfe ya hallaka wata Uwargida a babban birnin tarayya Abuja

Kaico! Injin surfe ya hallaka wata Uwargida a babban birnin tarayya Abuja

Wata Uwargida mai suna Hadiza ta gamu da ajalinta a lokacin da ta kai surfe, a kauyen Rubochi dake cikin garin Kuje kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Larabar data gabata da misalin kafe hudu na yamma, kamar yadda wani shaidan gani da ido ya bayyana ma majiyar Legit.ng, shaidan mai suna Jethro Samule ya bayyana cewar Hadiza ta kai surfe ne garin Rubochi daga kauyen Pesu.

KU KARANTA: Dakarun Sojin Najeriya sun yi caraf da wani Dan kunar bakin wake a Adamawa (Hotuna)

Samuel yace Uwarguda Hadiza ta durkusa don daukar kwanon dake dauke da masarar data kai nika da nufin mika shi ga mai nikan, sai kwatsam igiyar injin nikan ya kama mata Hijabi, ya ja ta har kan injin surfen, nan da nan ya fille mata kai.

A cewar Jethro, ganin haka ya sanya sauran matan dake layin surfe suka ranta ana kare, gudun idan baka yi bani wuri, daga bisani yan uwan Hadiza sun dauke gawarta, inda suka yi mata Jana’izah.

DPO na Yansandan yankin, CSP John Kareem ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin hatsari, sa’annan ya shawarci mata masu sanya Hijabai da su dinga kula musamman idan sun je ire iren wuraren nan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng