Kachikwu ya maida wa Falana martani akan makudan kudin tallafin mai

Kachikwu ya maida wa Falana martani akan makudan kudin tallafin mai

- A ranar Larabar nan ne karamin ministan man fetur na kasa, Ibe Kachikwu, ya maida martani ga babban lauyan nan mai kare hakkin 'dan adam, Femi Falana, wanda ya bukaci gwamnati tayi masa bayani yanda kudin tallafin mai ya tashi daga naira biliyan 261 duk shekara yayi tsalle zuwa Naira tiriliyan 1.4

Kachikwu ya maida wa Falana martani akan makudan kudin tallafin mai
Kachikwu ya maida wa Falana martani akan makudan kudin tallafin mai

A ranar Larabar nan ne karamin ministan man fetur na kasa, Ibe Kachikwu, ya maida martani ga babban lauyan nan mai kare hakkin 'dan adam, Femi Falana, wanda ya bukaci gwamnati tayi masa bayani yanda kudin tallafin mai ya tashi daga naira biliyan 261 duk shekara yayi tsalle zuwa Naira tiriliyan 1.4.

DUBA WANNAN: Duba Wurare hudu da Trump da Buhari suka yi kamanceceniya da juna

A bada amsar Kachikwu ya musanta maganar, ya kuma kirata da abin mamaki.

"Na samu wasikar ka mai kwanan wata 17 ga Afirilu, 2018 inda ka bukaci bayani. Ni dai ban fadi haka ba kuma akwai shaida da ta tabbatar da hakan. Bayanin da kayi ba daidai bane kuma hasashe ne kawai," inji Kachikwu.

Ministan ya fadi hakan ne a bainar jama'a cewa "Lokaci yayi da Najeriya zata fito da sabuwar hanyar samun mai kamar LPG a matsayin hanyar rage shigo da man fetur da kuma saida fetur a kudin da gwamnati ta yanke na N145 akan lita daya."

A cikin amsar da ya bawa Falana, Kachikwu yace matatar man fetur ta kasa ita ce zata san ko nawa ne kudin tunda su suke shigo da fetur din da ake siyarwa a Najeriya.

Wata daya kafin maganar Kachikwu, Shugaban matatar man fetur ta kasa Maikanti Baru, yace tallafin mai ya kai Naira miliyan 774.

Yace man fetur din da ake amfani dashi a rana lita miliyan 35 amma yanzu ya kai sama da lita miliyan 60.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng