Mutuwar Wani 'Dalibi 1 ta sanya an rufe wata Jami'a a jihar Kano

Mutuwar Wani 'Dalibi 1 ta sanya an rufe wata Jami'a a jihar Kano

Hukumomin jami'ar kimiyya da fasaha dake garin Wudil ta jihar Kano, ta bayar da umarnin rufe ta har na tsawon makonnin biyu yayin da daliban ta suka gudanar da zanga-zanga sakamakon mutuwar wani dalibi guda a ranar Larabar da ta gabata.

Wannan mamaci wanda kafin mutuwar sa dalibin aji uku ne, Faruk Abubakar, ya riga mu gidan gaskiya sakamakon dilmiyewa da ya yi a cikin babban Kogi na garin Wudil.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, shugaban jami'ar Farfesa Shehu Alhaji-Musa, shine ya bayar da wannan sanarwa yayin ganawa da manema labarai a ranar yau ta Alhamis.

Shugaban ya bayyana cewa, majalisar jami'ar ta kaddamar da ranar yau ta Alhamis da kuma gobe Juma'a a matsayin ranakun hutu ga daliban domin gudanar da jimamin dan uwan su da ajali ya katsewa hanzari.

Mutuwar Wani 'Dalibi 1 ta sanya an rufe wata Jami'a a jihar Kano
Mutuwar Wani 'Dalibi 1 ta sanya an rufe wata Jami'a a jihar Kano

Daga bisani kuma daliban za su shiga hutu na tsawon makonnin biyu kamar yadda hukumar makarantar da gindaya, inda ta nemi daliban da su gaggauta tattara komatsan su kuma su fice kafin yammacin ranar Alhamis din ta yau.

Ya kara da cewa, daliban sun gudanar da zanga-zanga sakamakon rashin dan uwan su da suka yi inda a yayin haka suka barnatar da wasu kayayyakin makarantar.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta cafke mutane 10 da laifin kai farmaki Gidan Hadimin Gwamna Bagudu

Legit.ng ta fahimci cewa, dalibai uku na jami'ar ne su tafi iyo a wannan babban Kogi duk da gargadin su da masu gadi suka yi amma giggiwa ta dalibai ta sanya su kayi masu kunnen uwar shegu.

A yayin haka ne biyu cikin wannan dalibai suka tsallake rijiya da baya sakamakon ceto da suka samu, inda kawowa yanzu dalibin guda an rasa ko da gawar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: