Bukola Saraki yayi tuntube ya soki Shugaban kasa Buhari a Tuwita

Bukola Saraki yayi tuntube ya soki Shugaban kasa Buhari a Tuwita

A makon nan ne wani abin kunya ya faru a Najeriya inda Shugaban Majalisar Dattawa watau Bukola Saraki yayi tuntuben sukar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafin sa na sadarwan zamani.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wani bayani a shafin sa na Tuwita inda yake yabawa gudumuwar da Kasar Amurka ta ke ba Najeriya tun lokacin yana gidan Soja. Sai dai martanin Bukola Saraki bai zo da dadin gani ba.

Bukola Saraki yayi tuntube ya soki Shugaban kasa Buhari a Tuwita
An samu bacin rana an kama Hadiman Saraki sun soki Buhari

Shugaban Majalisar Datttawan kasar Bukola Saraki a shafin sa na Tuwita ya maidawa Shugaban kasar amsa inda ya nuna cewa bai san komai ba. Sai dai kafin ayi wata-wata aka yi maza aka goge wannan magana da aka yi amma an makara.

KU KARANTA: Kamanceciniya 4 tsakanin Shugaban Amurka da Buhari

Ba mamaki wani daga cikin Hadiman Saraki ne yayi wannan baram-barama inda yayi tunanin cewa yana kan shafin sa ne kurum sai ya aika sako da sunan Shugaban Majalisar kasar. Wasu dai sun yi wuf sun dauki hoton abin da ya wakana.

Tuni dai na-kusa da Shugaban Majalisar su ka karyata cewa an soki Shugaban kasa Buhari inda su ka zargi Kayode Ogundamisi da kokarin lauya na’urorin zamani domin batawa Bukola Saraku suna. Sai dai wasu da dama sun ga wannan sako.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng