Matan Najeriya sun gindaya wasu sharuda 8 kafin goyan bayan duk wani mai son kuri'ar su a 2019

Matan Najeriya sun gindaya wasu sharuda 8 kafin goyan bayan duk wani mai son kuri'ar su a 2019

Wata kuniyar siyasa na mata mai suna League of women voters in Nigerian (LWVN) sun gindaya wasu manyan sharruda ga dukkan jam'iyyun siyasa a Najeriya kafin zaben 2019. Kungiyar na bukatar a tsayar da mataimakiyar shugaban kasa tare da bawa matan 35% na mukaman siyasa.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar, Dr. Esther Uduehi ta aike wa Daily Post a ranar Alhamis, kungiyar ta bukaci dukkan jam'iyyun siyasa su tsayar da mata guda 12 a matsayin 'yan takarar gwamna a jihohi 12, sannan dukkan sauran gwamnonin jihohi su tsayar mata a matsayin mataimakansu.

Babbar Magana: Matan Najeriya sun gindaya wasu sharuda 9 kafin goyan bayan don wani mai son kuri'ar su a 2019
Babbar Magana: Matan Najeriya sun gindaya wasu sharuda 9 kafin goyan bayan don wani mai son kuri'ar su a 2019

Kamar yadda yake a cikin sakon, ga bukatu guda takwas da kungiyar ta gabatar;

1) Dukkan wata jam'iyya da zata tsayar dan takara namiji ta tsayar da mace a matsayin mataimakiyarsa

2) Dukkan jam'iyyu su tsayar da 'yan takaran gwamna mata a kalla a jihohi 12 a Najeriya

3) Dukkan gwamnoni maza su tsayar da mata a matsayin mataimakansu

KU KARANTA: Ana zargin wani dan shekaru 55 da laifin yi wa yaro dan shekaru 8 fyade a Kano

4) Idan ba muyi nasarar samun shugaban kasa ko mataimakiyar shugaban kasa ba, muna bukatar kujerar sakataren gwamnati a matsayin tarayya da na jihohi

5) Muna bukatar a fitar kowace jihar ta fitar da Sanata mace guda daya a cikin Sanatoci uku da kowace jiha ke dashi

6) Muna bukatar kowace jihar ta fitar da mata biyu a matsayin 'yan majalisar wakilai

7) Muna bukatar a mace zabi mace tayi jagoranci a majalisar wakilai ko dattawa, kazalika, muna bukatar a raba mukamman majalisar tsakanin maza da mata

8) A majalisun jihohi, muna bukatar a zabi mata a kalla 12 a matsayin kakakin majalisa tare da bawa mata kashi 35% na mukamman majalisar jihohin.

Kungiyar tace tana bukatar a kara inganta rayuwar 'yan Najeriya musamman mata da matasa kuma tayi imanin cewa mata ne sukafi dace wa da gudanar da ingantaciyyar democradiyya tare da kawo canji mai ma'ana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164