Shettima da Sheriff sun amince zasu tsayar da gabar dake tsakaninsu

Shettima da Sheriff sun amince zasu tsayar da gabar dake tsakaninsu

- Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima na jam’iyyar APC sun samu matsaya na amince da tsohon gwamnan jihar ta Borno Sanata Ali Modu Sheriff da mutanensa su dawo cikin tafiyar tasu jam’iyyar

- An samu matsayar ne bayan taron tattaunawa da suka gudanar daga shekaranjiya Talata zuwa jiya wanda Gwamnan na jihar Borno Kashim Shettima da Sanata Ali Modu Sheriff da abokin tafiyarsa Alhaji Kashim Imam jigogin taron Malam Abba Kyari da Ambassador Babangida Kingibe suka halarta

- A kashen taron gwamna Kashin Shettima da tsohon gwamnan Ali Modu Sheriff sun gafartawa juna

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima na jam’iyyar APC sun samu matsaya na amince da tsohon gwamnan jihar ta Borno Sanata Ali Modu Sheriff da mutanensa su dawo cikin tafiyar tasu jam’iyyar ta APC.

An samu matsayar ne bayan taron tattaunawa da suka gudanar daga shekaranjiya Talata zuwa jiya wanda Gwamnan na jihar Borno Kashim Shettima da Sanata Ali Modu Sheriff da abokin tafiyarsa Alhaji Kashim Imam jigogin taron Malam Abba Kyari da Ambassador Babangida Kingibe suka halarta.

Taron wanda aka gudanar a karkashin jagorancin jami’in shugaban kasa Malam Abba Kyari kuma aka gudanar dashi a gidan Ambassador Babangida Kingibe da Asokoro, wanda a kashen taron gwamna Kashin Shettima da tsohon gwamnan Ali Modu Sheriff sun gafartawa juna.

Shettima da Sheriff sun amince zasu tsayar da gabar dake tsakaninsu
Shettima da Sheriff sun amince zasu tsayar da gabar dake tsakaninsu

Abubuwa muhimmai biyu da suka shawarta akai sune Ali Modu Sheriff da jama’arsa zasu iya dawowa jam’iyyar tasu ta APC tare da bin dokar jam’iyyar, sannan an amince da cewa al’amuran mazaba dana kananan hukumomi zasu cigaba da tafiya kamar yadda dokar jam’iyya ta tsara.

KU KARANTA KUMA: Dan takarar shugaban kasa ya shawarci mata da karda su yarda su tara da mazajensu idan har basu da katin zabe

Daya daga cikin manyan ‘yan siyasa dake tare da gwamnan jihar ta Borno, ya bayyanawa Daily Trust cewa tabbas an gudanar da taron a gidan Kingibe,don samun zaman lafiya tsakanin dattawan jihar musamman a ikin halin da ake na rikicin Boko Haram dake addabar jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng