Ban gama cika alkawuran da na dauka a 2015 ba – Shugaba Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa har yanzu fa akwai sauran aiki gaban sa a Najeriya. Shugaban kasar ya bayyana wannan ne a farkon makon nan lokacin da yake hira a Rediyo a Kasar Amurka.
Shugaban kasar ya kai ziyara har fadar Shugaban kasar Amurka a makon nan inda bayan nan yayi magana da ‘Yan jaridan VOA na kasar. Shugaba Buhari yace har yanzu ba a gama da yakin 'Yan ta'dda a Najeriya ba .
A lokacin da aka tambayi Shugaban game da shirin da yake yi na zaben 2019 ganin ya nuna niyyar zarcewa, ya bayyana cewa har yanzu Gwamnatin sa ba ta gama cika alkawuran da ta dauka ba a kan harkar tsaron kasar.
KU KARANTA: Wani Gwamna ya nemi a bi a hankali game da batun karin albashi
Shugaba Buhari yace ko da yake Boko Haram ba su da karfin karbe Garuruwa amma su kan jefa yara kanana su fita daga hayyacin su domin su tada bam a cikin Jama’a. Shugaban yace amma Sojoji sun rutsa Boko Haram a Sambisa.
A hirar Shugaban kasar da VOA a Ranar Talata yace ‘Yan Boko Haram su na cigaba da kai ragon hari a kasuwanni da coci da sauran su don haka har yanzu akwai sauran yaki da ‘Yan ta’addan a kasar duk da kokarin da aka yi a Gwamnatin sa.
Kun ji labari cewa Attajirin Afrika Aliko Dangote ya bayyana cewa zuwa karshen watan Satumba na shekarar nan Najeriya za tayi zarra a bangaren fita da takin zamani a kaf Nahiyar Afrika.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng