Najeriya za ta ciri tuta a bangaren takin zamani a 2018 – Dangote

Najeriya za ta ciri tuta a bangaren takin zamani a 2018 – Dangote

- A karshen shekarar nan za a ga canji kan harkar noma a Najeriya

- Aliko Dangote yace zuwa watan Satumba ne takin zamani zai yadu

- Dangote yace sai Najeriya ta zama gaba wajen fitar da taki a Afrika

Mun samu labari cewa Attajirin Afrika Aliko Dangote ya bayyana cewa zuwa karshen watan Satumba na shekarar nan Najeriya za tayi zarra a bangaren fita da takin zamani a kaf Nahiyar Afrika.

Hamshakin ‘Dan kasuwan na Duniya Dangote yace Kasar Najeriya za ta zama ta farko wajen fita da takin noma na zamani zuwa kasashen waje a Afrika. Aliko Dangote yace ana ganin canji a Gwamnatin Shugaba Buhari.

Najeriya za ta ciri tuta a bangaren takin zamani a 2018 – Dangote
Dangote yayi wa 'Yan Najeriya albishir a harkar noma

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da manyan masu harkar noman da ake ji da su a Kasar Amurka lokacin da ya kai ziyara kwanan nan. Akiko Dangote da John Coumantaros su na cikin wanda su ka halarci zaman.

KU KARANTA: Gwamna Fayose yayi kaca-kaca da wasu Gwamnonin APC

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na kokari wajen ganin Najeriya ta noma abin da za ta ci a gida. Gwamnatin dai dama tayi alkawarin maida hankalin al’umma kan harkar noma da habaka tattalin kasa da samar da tsaro.

Dangote yayi wa 'Yan Najeriya albishir a harkar noma yace tuni dai har an fara ganin canji a kasar. Dama dai Gwamnatin Shugaba Buhari ta shiga yarjejeniya da kasar Morocco domin inganta harkar hada takin zamani a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel