Hauwa Maina ta rasu, karanta wasu muhimman bayanai game da ita guda 8 da baka sani ba
A ranar Talata 2 ga watan Afrilu ne Kannywood ta yi gamu da rashin fitacciyar jaruma, Hauwa Maina, wanda ta rasu a Asibitin Malam Aminu Kano bayan karamar jinya da ta yi, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
A nan Legit.ng ce ta kawo muku wasu muhimman abubuwa guda 5 game da marigayiya Hauwa Maina:
KU KARANTA: Yadda wasu daliban Fimari su 6 suka tsallake rijiya da baya yayin da suka afka cikin Masai
1- Hauwa Maina ta fara fitowa a fina finai ne a shekarar 1999
2- Kamfanin Saminu Mohammed Mhamud ne ta shirya Fim din da ta fara fitowa a cikinsa shi
3- Hauwa Maina ta yi suna sosai a kwakwaiyon Sarauniya Amina da Bayajida
4- Hauwa Maina ta kwashe kusan shekaru 20 tana harkar Fima
5- Baya da fina finan Hausa, Hauwa tana fitowa a Fina finan Turanci wato Nollywood
5- Hauwa Maina ta yi karatu a Kwalejin gwamnatin tarayya na Kimiyya da fasaha na Kaduna
7- Hauwa Maina ta lashe manyan kyautuka da suka hada da Fitacciyar Jaruma na SIM Awards, kyautar Best Afro Nollywood London, 2007.
8- Har zuwa rasuwarta, Hauwa Maina ma’aikaciya ce a gidan Rediyon Liberty, kuma tana koyarwa a cibiyar koyar da harshen Turanci na Kabiru Jammaje dake Kaduna.
Ana sa ran za'a yi mata jana'iza a ranar Alhamis 3 ga watan Afrilu a garin Kaduna.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng