Rikicin Benuwe: An kama wani dauke da muggan makamai a jihar Benuwe

Rikicin Benuwe: An kama wani dauke da muggan makamai a jihar Benuwe

- Rundunar sojin Najeriya tace ta kama Idi Gemu a kauyen Adagu dake karamar hukumar Guma ta jihar Benue dauke da bindiga kirar AK 47

Rikicin Benuwe: An kama wani dan ta'adda dauke da muggan makamai
Rikicin Benuwe: An kama wani dan ta'adda dauke da muggan makamai

Rundunar sojin Najeriya tace ta kama Idi Gemu a kauyen Adagu dake karamar hukumar Guma ta jihar Benue dauke da bindiga kirar AK 47.

Shugaban rundunar Sojin, Lt. Col Suleiman Mohammed yayi hira da manema labarai a jiya. Inda yake cewa sun kama wanda ake zargin ne lokacin da suke aiki a karamar hukumar.

DUBA WANNAN: A fara hana mulkin kama karya a Najeriya, maimakon hana shan Kodin - Ben Bruce

Kamar yanda yace, rundunar ta kama makiyaya uku da ake zargi a makon da ya gabata a Tormatar a karamar hukumar Guma.

"Rundunar mu ta kama makiyaya uku a makon da ya gabata a Tormatar, bayan tsananta bincike da muka yi mun samu hanyar da muka kama shima wannan makiyayin. A kokarin da muke na ganin mun kare rayuka da dukiyoyi al'umma, kuma muna rokon jama'a da su dinga bamu hadin kai don kawo karshen ta'addancin. "

Ya bayyana cewa akwai wata kullaliyar dangantaka tsakanin mutane uku na farkon da suka kama da kuma Idi Gemun ganin cewa binciken su hakan ya nuna.

Amma a lokacin da aka tambaya waye ya dau nauyin ta'addancin sai yace "A yanzu da bazan iya ansa wannan tambayar ba."

A hirar da manema labarai sukayi da wanda ake zargi, Idi Gemu, yace shi dan asalin jihar Nasarawa ne a garin Adudu. Yazo neman tumakinshi ne da suka bace, sai kawai sojoji suka kama shi.

"Bindigar ba tawa bace, ta abokina ce da na kwana gurin shi bayan naga tumakina a gurin wasu fulani makiyaya dake zama a nan Benue. "

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel