Shugaba Buhari ya bayyanawa mutanen Najeriya wani sirrin rayuwarsa cewa baya sauraren waka

Shugaba Buhari ya bayyanawa mutanen Najeriya wani sirrin rayuwarsa cewa baya sauraren waka

- Abubuwa kadan ne aka sani game da rayuwar shugaba Buhari banda kaunar da yake yiwa shanu da kuma son karanta jaridar zanen kamar yadda mai magana da yuwansa ya bayyana Shehu Garba

- Shugaban kasar ya dan bayyana wani sirrin rayuwarsa, inda ya bayyana cewa baya sauraron waka

- Shugaba Buhari yace baya sauraren waka amma yana samun lokaci don ya huta

Abubuwa kadan ne aka sani game da rayuwar shugaba Buhari banda kaunar da yake yiwa shanu da kuma son karanta jaridar zane kamar yadda mai magana da yuwansa Shehu Garba ya bayyana.

Shugaban kasar ya dan bayyana wani sirrin rayuwarsa, inda ya bayyana cewa baya sauraron waka, hakan ya fito ta hanyar Aliyu Mustapha jami’in Voice of America, a Washington DC, a ranar Talata lokacin da yake zantawa da shugaban kasar.

Shugaban Buhari ya bayyanawa mutanen Najeriya wani sirrin rayuwarsa cewa baya sauraren waka
Shugaban Buhari ya bayyanawa mutanen Najeriya wani sirrin rayuwarsa cewa baya sauraren waka

Shugaba Buhari yace “bana sauraren waka amma ina samun lokaci don na huta. Lokacin da nake Janar na soja nike bayar da umurni, amma yanzu, ni ake bawa umurni. Ga likitana nan ko yaushe cewa yakeyi naci abinci mai kyau na huta, shiyasa mutane dayawa ke mamakin yanda na warke cikin sauri.”

Buhari ya dauki tsawon kwanaki 100 yana jinyar ciwon da ba’a bayyanawa duniya ba a kasar Ingila a shekarar 2007, wanda har wasu ke fadar cewa bazaya iya tafiyar da aikinsa ba yanda ya kamata, wanda daga baya ya dawo Najeriya kuma yake da lafiya tun lokacin.

KU KARANTA KUMA: Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a harin da aka kai a masallacin Najeriya ya kai 86

Ba kamar magabacinsa ba Goodluck Jonathan da matarsa Patience wadanda suke kaunar masu nishadantarwa musamman ‘yan wasan film na Nollywood, hakan na nuna cewa Buhari yana da abubuwan da sukafi damunsa da suka fi nishani.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa a farkon makon nan ne dai shugaba Buhari ya dawo daga kasar Amurka bayan amsa gayyatar da shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi masa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel