Majalisa na goyon bayan karin albashi mafi karanci ga ma'aikatan Najeriya - Dogara

Majalisa na goyon bayan karin albashi mafi karanci ga ma'aikatan Najeriya - Dogara

Kakakin Majalisar Wakilai, Dogara Yakubu, ya kara jadada cewa Majlisar a shirye ta ke ta amince da kudirin karin mafi karancin albashin ma'aikata zuwa ga Majalisar Dattawa don amincewa dashi.

A jawabin da yayi a ranar bikin ma'aikata na 2018, Dogara ya ce Majalisar na jira ne kawai sashin shugaban kasa ta aiko da kudirin dokar su kuma su tattauna a kan ta kuma su amince dashi.

Dogara ya ce yana sana da irin kallubale da wahalwalun da ma'aikatan Najeriya ke fuskanta hakan yasa Majalisar Wakilan za tayi duk mai yiwuwa don ganin cewa an kara inganta rayuwar ma'aikatan.

Majalisa a shirye take ta amince da kudirin karin mafi karancin albashi - Dogara
Majalisa a shirye take ta amince da kudirin karin mafi karancin albashi - Dogara

DUBA WANNAN: Majalisar zartarwa ta ware N245bn don gina tituna da wasu muhimman aiki - Fashola

Dogara ya ce a halin yanzu kwamitin gwamnatin duba karin albashin suna gudanar da taron jin ra'ayin mutane a dukkan yankuna shida na Najeriya kuma daga baya zasu tattara bayanansu su mika zuwa shugaban kasa kuma ya aike ma Majalisar don su amince dashi.

"A madadin mambobin Majalisar wakilai, ina son inyi amfani da wannan damar in kara jadada muhimmancin da ma'aikatan Najeriya ke dashi wajen cigaban kasar.

"Muna ganin irin kallubalen da kuke fama dashi kuma mun san cewa albashin ku baya sati daya. Muna ganin yadda kuke bayar da gudunmawar ku wajen tafiyar da ayyuka lami lafiya duk da irin mawuyacin halin da kuke fuskanta. Muna muku jinjina kuma muna rokonku ku cigaba da baya gwamnati goyon baya.

"Muna tabbatar muku da cewa da zarar an tura kudirin karin albashin zuwa Majalisa zamu yi gagawan amincewa dashi har ma da duk wata kudiri da zata kara jin dadi da walwalan ma'aikata," Inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164