Majalisar zartarwa ta ware N245bn don gina tituna da wasu muhimman aiki - Fashola

Majalisar zartarwa ta ware N245bn don gina tituna da wasu muhimman aiki - Fashola

Bayan korafe-korafen da gwamnonin wasu jihohi suka rika yi ga gwamnatin tarayya, Majalisar Zartarwa na kasa a jiya ta amince da fitar da kudi N105bn saboda karasa ayyukan gina tituna 44 a jihohin Najeriya.

A taron da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinanjo ya jagoranta na tsawon sa'o'i takwas, majalisar kuma ta ware N80.199bn a matsayin kudin da za'ayi amfani dashi don karasa ginin titin Legas-Ibadan mai tsawon kilomita 84.

Majalisar zartarwa ta ware N245bn don gina tituna da wasu muhimman aiki
Majalisar zartarwa ta ware N245bn don gina tituna da wasu muhimman aiki

Majlisar kuma ta amince da ware N38.034bn saboda ginin titi mai tsawon kilomita 72 da ke hanyar Orikam a jihar Enugu. Za'a fitar da kimanin kudi N10bn daga cikin asusun muhalli na Ecological Fund don biyan kwangilar da aka baiwa kamfanin RCC Limited.

DUBA WANNAN: Ku kalli ayyuka har 109 da shugaba Buhari zai dasa a jihar Zamfara

Ministan Ayyuka, Makamashi da Gidaje, Babatunde Fashola ya fadawa manema labarai na gidan gwamnati cewa Majalisar da ware N18.874bn saboda gyaran gadan Third Mainland Bridge.

Ministan ya ce duk da cewa gwamnatin da ta wuce ne ta bijiro da aikin ginin gadan, sai dai bata ware kudi a kasafin kudin kasa ba don gudanar da aikin. Ya kuma ce Majalisar ta ware kudi N2.5bn don sake fasalin gadan Illie da ke jihar Osun.

Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi, kuma ya ce Majalisar Zartarwa ta fitar da kudi na gyaran layin dogo saboda kara gudun jiragen kasa da kuma N1.2bn saboda siyan tarago da wasu jiragen.

Ameachi ya ce Majalisar ta kafa wata kwamiti na musamman da zasu sa ido kan aikin ginin titin East-West, mambobin kwamitin sun hada da Ministan Harkokin Neja-Delta, Ministan Ayuka da gidaje da kuma Minitan Labarai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164