Yan bangan siyasa sun kai ma wani na hannun daman gwamnan jihar Kebbi farmaki
Rundunar Yansandan jihar Kebbi sun tabbatar da kama wasu mutane 10 da suke zarginsu da bangan siyasa, bayan samun wani rahoto dake nuna sun kai ma wani hadimin gwamnan jihar Kebbi, Faruk Enabo farmaki a gidansa, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Kaakakin rudunar Yansanda jihar Kebbi, Mustapha Suleiman ne ya sanar da haka a ranar Laraba 2 ga watan Mayu, a Birnin Kebbi, inda yace harin ya samo asali ne sakamakon rikicin siyasa daya kaure a tsakanin magoya baya.
KU KARANTA: Fitaccen mawakin Kannywood ya tabbatar da soyayyarsa ga shahararrar Jaruma, Gabon
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin yana cewa matsalar ya faru ne a tsakanin kungiyoyin magoya bayan gwamnan jihar guda biyu, Buhari-Bagudu Support Organisation, BBSO, da 4+4 Buhari Bagudu Continuity Organisation.
Suleiman yace magoya bayan guda daga cikin kungiyoyin ne suka kai ma Faruk hari a gidansa dake birnin Kebbi dauke da muggan makamai, har ta kai ga sun lalata masa motoci tare da illata Maigadin gidan.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng