Cikin Hotuna: Wata Kungiyar Matasa ta tallafawa Marayu kayan Makaranta a jihar Kano
Wata sabuwar Kungiyar Matasa mai lakabin JYDA (Janbulo Youths Development Association), ta bayar da tallafin kayan makaranta na sama da N100, 000 ga kimanin marayu 80 a unguwar Dorayi dake karamar hukumar Gwale ta jihar Kano.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan abin son barka da kungiyar ta aiwatar ya zo ne domin agazawa masu karamin karfi musamman marayu akan harkokin su na karatu da neman ilimi.
A yayin gabatar da wannan tallafi ga Mai Unguwar Dorayi Babba, Mallam Badamasi Bello, shugaban kungiyar Abdulfatah Magaji tare da babban sakataren kungiyar Yusuf Ali Yusuf, sun bayyana damuwar su dangane da halin da masu karamin karfi ke tsintar kansu yayin neman ilimi a yankin.
A sanadiyar haka ne jiga-jigan kungiyar suka kirayi masu hannu da shuni da masu karfi cikin al'ummar yankin da ma jihar Kano baki daya akan su zuba hannayen jari da zasu kwashi riba gobe kiyama wajen tallafawa kanana yar da suke tsintar kawunan su cikin halin kakanikayi yayin neman ilimi.
KARANTA KUMA: Wani Hatsarin Mota ya salwantar da rayuwar Sufeton 'Yan sanda a jihar Ogun
A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Kansila na Unguwar ta Dorayi Mallam Jibrin Mu'azu, ya yabawa wannan kungiya ta JYDA tare da jinjina a gare ta dangane da hobbasan da aiwatar.
Ya kara da cewa, da za a samu wasu kungiyoyi da za su yi koyi da ita tabbas ci gaba zai bunkasa ta fuskantar ilmantar da kananan yara wajen samun makoma ta gari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng