Tashin bam: Za mu matsawa Gwamnati ta tashi tsaye – Shehu Sani

Tashin bam: Za mu matsawa Gwamnati ta tashi tsaye – Shehu Sani

- Shehu Sani yayi tir da harin kunar bakin waken da aka kai jiya

- Sanatan ya bayyana yadda za ayi maganin wannan bala’i a kasar

- Mutane sama da 20 bam ya kashe a masallaci jiya a Garin Mubi

Wani ‘Dan Majalisar Dattawa da ka karkashin Jam’iyyar APC yayi magana bayan bam din wasu ‘yan kunar bakin-wake ya kashe jama’a a Garin Mubi a Jihar Adamawa inda yace za su nemi Gwamnati ta kara kokari kan harkar tsaro.

Tashin bam: Za mu matsawa Gwamnati ta tashi tsaye – Shehu Sani
Shehu Sani da ke karkashin Jam’iyyar APC mai mulki a Majalisar Dattawa

‘Dan Majalisar na Jihar Kaduna Sanata Shehu Sani ya bayyana hanyoyi 3 da za a bi wajen inganta tsaro a Yankin na Arewa-maso-gabas da daukacin kasar gaba daya lokacin da yayi tir da wannan hari a shafin sa na Tuwita.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta dauki yaki da barayi gadan-gadan

Shehu Sani wanda ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar kasar yace za su yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta rika amfani da na’urar da ke gane bam a Makarantu da Masallatai da coci na kasar domin kawo karshen bala’in.

Bayan nan kuma Sanatan yake cewa za su nemi Gwamnatin Tarayya ta sa a rika amfani da na’u’rorin daukar hoto a Dakunan Ibada da kuma Makarantu. Hakan zai sa a inganta harkar tsaro a wuraren da jama’a ke taruwa.

Har wa yau ‘Dan Majalisar yace akwai bukatar a horar da Malaman addini game da sha’anin tsaro domin kawo karshen rashin rayuka a dalilin ‘Yan ta’addan Boko Haram. Kun ji cewa harin bam din yayi sanadiyar mutane da dama jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: