Ko an kara albashi a Najeriya an yi banza idan har … Inji Masari

Ko an kara albashi a Najeriya an yi banza idan har … Inji Masari

- Masari yace Ma’aikata su nemi a gyara harkar ilmi da kiwon lafiya

- Gwamnan yace fa ya kamata a duba wadannan kafin karin albashi

- Ma’aikata na neman a maida mafi karancin albashi ya zama N56000

Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya nemi ayi la’akari da wasu mihimman abubuwa kafin a fara maganar karin albashi a Najeriya. Irin wadannan abubuwa kuwa su ne kiwon lafiya da irin su ilmi.

Ko an kara albashi a Najeriya an yi banza idan har … Inji Masari
Gwamnan Katsina ya nemi a bi a hankali game da batun karin albashi
Asali: Twitter

Mai Girma Gwamnan na Katsina yayi wannan kira ne lokacin da yake jawabi ga ‘Yan kwadago a fadin Jihar a jiya. Gwamnan yace ka da Ma’aikatan su karkata game da batun karin albashi kurum su kuma rabu da sauran sha’anin Gwamnati.

KU KARANTA: Buhari yace an kashe mutane ya fi a kirga a Zamfara

Rt. Hon. Aminu Masari yace idan har ba a gyara harkar ilmi da tsarin kiwon lafiya da noma da sauran su ba dai ko da an kara albashi an yi aikin banza ne. Yace idan ba a duba sauran abubuwan ba haka za ayi ta neman karin albashi kullum.

Lokacin da yake na sa jawabin, Tanimu Saulawa wanda shi ne Shugaban ‘Yan kwadago na Jihar ya dai nuna cewa yana sa rai zuwa tsakiyar shekarar nan Ma’aikata su fara karbar albashin da akalla ya kai N56000 zuwa N66500 a Najeriya.

Jiya Rt. Hon. Yakubu Dogara a wani jawabi da yayi ya bayyana cewa Majalisar Wakilan Tarayya a shirye ta ke tayi na’am da kudirin kara albashin Ma’aikata da zarar ya zo daga Shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng