Jerin barayi: Dokpesi ya kai Ministocin Shugaba Buhari gaban Alkali
- Raymond Dokpesi ya maka Gwamnatin Tarayya a gaban Kotu
- Ana dai zargin Dokpesi da satar kudin da su ka haura Biliyan 2
- Dokpesi yace sharri ake yi masa don haka yace a dauki mataki
Shugaban Kamfanin DAAR Raymond Dokpesi ya jibga Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a babban Kotun Tarayya a karshen watan jiya inda yake neman a biya shi makudan kudi na bata masa suna.
Mista Raymond Dokpesi ya kai Ministan yada labarai da Ministan shari’a na Gwamnatin Buhari watau Lai Mohammed da Abubakar Malami a gaban Alkali game da sunan sa da aka fito da shi cikin sunayen wadanda su ka saci kudin kasar.
KU KARANTA: Buhari ya so ne yayi bakam da Obasanjo bayan wasikar sa
Dokpesi ya shigar da kara ta bakin Lauyan sa Mike Ozekhome SAN bisa sharrin da aka yi masa na cewa ya saci Naira Biliyan 2.1 na kudin Gwamnati. Ozekhome yace dole a biya Biliyan 5 na bata masa suna da aka yi a gaban Duniya babu dalili.
Ko da dai ana Kotu yanzu da shi Shugaban na Kamfanin DAAR inda ake zargin sa da karkatar da dukiyar al’umma sai dai dai tuni ya musanya zargin da ke wuyan sa. Dokpesi ya kuma nemi Kotu ta dakatar da buga sunan sa da ake yi da laifin sata.
Jiya kun samu labari cewa Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta yi ram da tsohon Ministan sufurin jirgin sama Osita Chidoka game da wasu makudan kudi da ake zargin sa da yin gaba da su.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng