Da kamar wuya, gurguwa da auren nesa: Wani Gwamnan a Najeriya zai fara biyan ma’aikatan jiharsa kudin bacci

Da kamar wuya, gurguwa da auren nesa: Wani Gwamnan a Najeriya zai fara biyan ma’aikatan jiharsa kudin bacci

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya sanar da karin matsayi ga kafatanin ma’aikatan jihar Imo, bisa jajircewar da suke nunawa a bakin aiki, hadi da gudunmuwa da suke baiwa gwamnatinsa, kamar yadda jaridar The Cables ta ruwaito.

Gwamnan ya sanar da haka ne a bikin ranar ma’aikata ta Duniya da ya gudana a ranar Talata, 1 ga watan Mayu a dandalin jarumai dake babban birnin jihar Imo, Owerri, inda yace karin matsayin da ya yi ma ma’aikatan zai fanshe shekaru bakwai da suka yi a baya ba tare da karin matsayin ba.

KU KARANTA: Buhari ga Matasa: Ku rungumi sana’ar Noma domin ku tsira da mutuncinku

“Ina jinjina ma ma’aikatan jihar Imo bisa kokari da jajircewa da suke nunawa, duk da kalubalen tsaro, karancin albashi da rashin kayan aiki da suke fama da shi, ina sane da matsalolinku da bukatunku, don haka zan fara biyan ku kudin bacci.”

Da kamar wuya, gurguwa da auren nesa: Wani Gwamnan a Najeriya zai fara biyan ma’aikatan jiharsa kudin bacci
Rochas

Gwamnan ya tabbatar ma kafatanin ma’aikatan jihar Imo cewa ko nawa gwamnatin tarayya ta amince da shi a matsayin karancin albashi zai biyasu ba tare da bata lokaci ba, ya kara da cewa gwamnatinsa ta rage bashin kudi fansho da ake bin jihar daga naira biliyan 1.7, zuwa naira miliyan 700.

Daga karshe yayi kira ga ma’aikata da su yi rajistan katin zama dan kasa, don da haka ne kadai zasu zabi shuwagabannin da suke muradi, da zasu kare muradansu tare da biyan bukatunsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel