Lafiya jari: Anfani 5 masu ban mamaki da albasa ke da su a jikin dan adam
Albasa dai na daya daga cikin kayayyakin masarufin yau da kullum na al'umma musamman ma a wajen kayan hadin miya da ma dafa abinci baki daya da ke da matukar farin jini.
Albasa takan karawa abinci dandano da kuma kamshi mai dadin gaske wanda hakan ne ma ya sa dayawa daga cikin mutane suke anfani da ita sosai.
To sai dai baya ga karin dadi da kuma dandano abinci, albasar kamar yadda bincike ya tabbatar tana da da wasu tarin anfanin a jikin dan adam da da dama daga cikin al'umma basu sani ba.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin su kamar haka:
1. Tana maganin ciwalwatan hanyoyin fitsari.
2. Tana maganin cutar daji watau kansa.
3. Tana rage yawan suga a jikin dan adam.
4. Tana kara karfin garkuwar jikin dan adam.
5. Tana taimakawa jiki wajen karin sarrafa abinci.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng