Gwamnan jihar Kebbi ya jefa Yan fansho cikin halin farin ciki da biyansu naira biliyan 9

Gwamnan jihar Kebbi ya jefa Yan fansho cikin halin farin ciki da biyansu naira biliyan 9

Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu ya sanar da biyan kudaden fansho da na gratuti ga ma’aikatan da suka yi murabus daga aikin gwamnati su 3,500 na jihar Kebbi, da suka kai naira miliyan dubu tara, 9,000,000,000, inji rahoton Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne a yayin bikin ranar ma’aikata ta Duniya daya gudana a ranar Talata 1 ga watan Mayu, a filin taro dake Birnin Kebbi, wanda kungiyar kwadago reshen jihar ta shirya.

KU KARANTA: Yadda Hotunan aure suka janyo mutuwar wani aure kwana daya da daura shi

“Tun daga hawanmu mulki, mun biya ma’aikatan da suka bar aiki da adadinsu yah aura 3,500 hakkokinsu fiye da kudi naira biliyan tara, don haka ba zamu yi kasa a gwiwa ba wajen kara jajircewa da aikin da muka fara.” Gwamnan kenan a yayin da yake baiwa NLC tabbaci.

Gwamnan jihar Kebbi ya jefa Yan fansho cikin halin farin ciki da biyansu naira biliyan 9
Atiku

Bugu da kari gwamna Bagudu ya sanar da burinsa na ganin gwamnati da kungiyar kwadago sun cigaba da aiki tare don ganin sun janyo kananan yan kasuwa cikin tafiyar domin samun hadin kai mai daurewa, haka zalika ya yaba da goyon bayan da yake samu daga kungiyar.

A nasa jawabin, shugaban NLC reshen jihar Kebbi, Umar Halidu ya bukaci gwamnatin jihar ta duba yiwuwar karin kudin yan fansho musamman ga ma’aikatan da suka bar aiki a shekarar 2012 da 2013, duba da karin albashi da aka yi a wannan lokaci.

“Muna kira ga gwamnati ta cigaba da aiwatar da tsarin karin kudin fansho a duk shekara kamar yadda aka saba a baya, yau shekara takwas kenan da dakatar da wannan tsari, ya kamata a cigaba. Kuma ya kamata a samar da gidajen zama ga Malaman Firamari, musamman na kauyuka don kara musu kaimi.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng