Yadda Hotunan aure suka janyo mutuwar wani aure kwana daya da daura shi

Yadda Hotunan aure suka janyo mutuwar wani aure kwana daya da daura shi

Duk wanda yaki ji, baya ki gani ba, ko kuma ace duk wanda bai ji bari ba, ya ji hoho, kamar yadda bahaushe mai ban haushi yake fadi, a nan ma wani abin haushi, kuma abin takaici ne ya faru a tsakanin wasu sabbin ma’aurata, inda aurensu ya mutu bayan kwana daya rak da daura aure.

Gidan rediyon Dala FM na jihar Kano ne ya dauko wannan rahoto, inda yace aure wani Ango mai suna Jamilu, da Amaryarsa Badariyya, dukkaninsu mazauna garin Dawakin Tofa, ya mutu kwana daya da tarewar amarya sakamakon rikici da ya barke akan hotunan biki, wato Pre wedding Picture.

KU KARANTA: Sakin layi: Buhari ya bayyana akasarin matasan Arewa a matsayin jahilai

Jamilu ya saki Badariyya ne kan kin bin umarninsa, inda yace ma ta baya sha’awar daukar hotunan kafin aure, kuma ya tabbatar mata da cewa ba zasu yi ba, amma abinka da shaidanin dake tare da mata iyayen bidi’a, sai Amarya ya wancakalar da bukatar sahibinta, ba don bata son shi ba.

Duk da jan kunne da Jamilu Ango ya yi ma Badariyya, ashe ta zagaya, ta samu wani dan uwanta, wani kanin mahaifiyarta, suka sha hotunan tamkar Amarya da Ango, bakinsu kanin kafarsu, babu wanda ya sani, ya ji, ko ya gani.

Sai dai asirin Badariyya ya tonu ne a lokacin da kanin mahaifiyartata ya yi kasassabar daura hotunan a shafinsa na Facebook, don burgewa tare da nuna ma Duniya irin kyawun hoto, inda Jamilu Ango ya kicibus dasu, kuma ya sake ta kamar yadda Amaryar da kanta ta tabbatar ma majiyar Legit.ng.

Da aka tambayi Amarya me zata ce game da wannan lamari mara dadin ji, sai tace: “Ina baiwa mata shawarar su daina yin abin da mazansu suka hana su, don kuwa ga abin ya faru da ni.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel