Dan sandan Najeriya da bai taba karbar cin hanci ba ya samu kyauta daga BBC

Dan sandan Najeriya da bai taba karbar cin hanci ba ya samu kyauta daga BBC

Wani bincike da hukumar kididdiga ta kasa ta gudanar ya tabbatar da cewar jami'an 'yan sanda ne suka fi kowa cin hanci a Najeriya.

Saidai duk da wannan bakar shaida da aka yiwa 'yan sandan Najeriya, wani dan sanda guda daya tilo ya fita zakka.

Wani bincike ya bankado jami'in dan sanda, Julius Adedeji, da bai taba karbar cin hanci ba duk da kasancewar an sha kokarin bashi cin hanci amma bai taba karba ba.

Bisa wannan shaida da Adedeji ya samu ne kamfanin watsa labarai na BBC ya kararrama shi.

Dan sandan Najeriya da bai taba karbar cin hanci ba ya samu kyauta daga BBC
Dan sandan Najeriya, Julius Adedeji, da wakiliyar BBC

Da yake jawabi ga wakilin BBC bayan karbar kyautar sa, Adedeji, ya nuna mamakin sa tare da bayyana cewar bai san ana kula da abinda yake yi ba.

"Nagode Allah da samun wannan kyauta kuma zan kara dagewa da cigaba da kawar da kai daga duk nau'i na cin hanci," in ji Adedeji.

DUBA WANNAN: Jihar Imo ta karawa takarar Buhari armashi, karanta abinda ya faru

Da yake amsa tambayar ko an taba yunkurin bashi cin hanci, sai ya ce, "tabbas! Ko a yau wani ya yi kokarin bani kudi amma na ce masa bana karba. An sha gwada imani na ta hanyar kokarin bani kudi masu yawa. Ka san halin zuciya, amma dai ban taba karba ba."

Adedeji ya ce ya sha fada wa abokan aikin sa cewar indai kana yin aiki bisa gaskiya Allah zai yi maka sakayya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng