Jami'ar Musulunci ta dakatar da dalibai 23 bisa laifin Zina a cikin makaranta

Jami'ar Musulunci ta dakatar da dalibai 23 bisa laifin Zina a cikin makaranta

- Daya daga cikin shugabannin jami'ar, Dr. Sulait Kabali, wanda shine sakataren kwamitin ladaftarwa na jami'ar ya sanarwa da manema labarai a ranar Litinin dinnan cewa an kama daliban laifin zinar, inda kuma hakan na nuni da karya dokar makarantar

Jami'ar Musulunci ta dakatar da dalibai 23 data kama da laifin Zina a cikin makaranta
Jami'ar Musulunci ta dakatar da dalibai 23 data kama da laifin Zina a cikin makaranta

Daya daga cikin shugabannin jami'ar, Dr. Sulait Kabali, wanda shine sakataren kwamitin ladaftarwa na jami'ar ya sanarwa da manema labarai a ranar Litinin dinnan cewa an kama daliban laifin zinar, inda kuma hakan na nuni da karya dokar makarantar.

DUBA WANNAN: Kuyi da gaske don kawo karshen rashin tsaro a Najeriya - Soyinka ya gargadi gwamnatin tarayya

"An kama daliban da laifin aikata zina a makaranta, wanda ya sabawa dokar jami'ar."

Mista Kabali ya kara da cewa wasu daliban an kamasu da laifin sata, shan giya da kwayoyi, cikin shege da kuma haddasa rashin zaman lafiya a jami'ar.

A wasika wasika wacce aka fitar a ranar 14 ga watan Afirilu, 2018 wanda kafafen yada labarai suka gani, an kama daliban ne a lunguna masu duhu suna soyewa a lokaci daban daban.

"A sakamakon bincike da kwamitin ladaftarwa ta makarantar tayi, da kuma amsa laifinkan su da sukayi na aikata laifukan da ake tuhumar su dashi wanda kunsan ya sabawa dokar jami'ar, an bukaci da su dakata da karatu a makarantar."

Mista Kabali yace dakatarwan zai dau tsawon shekara daya ne, sannan ya zama Jan kunne ga daliban, cewa da hukumar makarantar bazata yi kasa a guiwa gurin korar duk dalibin da yayi ma doka karantsaye ba.

Cikin dakatattun daliban akwai 'yan ajin karshe, wadanda gab suke da rubuta jarabawar karshe.

An ba daliban wa'adin sati daya da su daukaka kara in sunga ba'ayi musu adalci ba.

Ms Rehema Katono, jami'ar hulda da jama'a ta makarantar ta jinjiinawa kwamitin ladaftarwar jami'ar inda tace nan ba da dadewa ba zata yanke ma daliban da suka daukaka kara hukunci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng