Asirin wata mata dake koyawa kwailaye karuwanci ya tonu
- An gurfanar da matar me suna Blessing Akwaram a babbar kotun Yaba akan tuhumar ta da akeyi da sanya wata budurwa yar shekaru 18 a karuwanci.
- An bada belin Blessing akan kudi miliyan N2
- An dage sauraran karar zuwa ranar Laraba 13 ga wata Yuni
A ranar Litinin 30 ga watan Afrilu babbar kotun majisatre da ke Yaba na jihar Legas ta bada belin wata mata akan kudi naira miliyan 2 bisa laifin kawalanci da takeyi ga kananan yara.
Alkalin kotun Majistare da ke Legas, O.G Oghere ya tabbatar da laifin inda yace dole Blessing ta kawo shaidu guda biyu sannan yace dole ne shaidun su bada wata shaida ta haraji na shekara uku a Legas.
Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta rawaito mana cewa ana zargin Akwaram da aikata laifuka uku da suka hada da safaran yara, cin zarafin yara, satan yara amma ta musanta aikata hakan.
KU KARANTA: Gwamnati ta haramta sarrafa maganin tari mai sinadarin kodin
Saja Modupe Olaluwoye ya bayyana kotu ce wadda ake zargin ta aikata laifin ne a ranar Litinin 2 Afrilu da misalin karfe 1:00 na rana.
Yace wadda ake zargin ta dauki wata yarinya me suna Aminat Akinbode mai shekaru 18 dan sata a harkar karuwanci. Ta samu nasarar tsere wa inda ta sanar da yan sanda dake Seme.
Hakan ya sabawa doka ta 411 a kundin laifuka na jihar Legas 2015 da section 24 da 26 na damar yara na Legas 2007.
Oghere ya daga sauraran karar zuwa ranar Laraba 13ga Yuni.
Legit.ng ta rawaito cewa hukumar NAPTIP ta kama wasu mutane biyu da aikata irin wannan laifin safarar yara daga Najeriya zuwa kasar Libya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng