Shugaba Buhari ya sake yin tsokaci akan matasan Najeriya

Shugaba Buhari ya sake yin tsokaci akan matasan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tsokaci akan jawabinsa game da matasan Najeriya wanda ya haifar da cece-kuce a kwanakin baya.

A cewar majiyarmu ta BBC Hausa, shugaban kasar ya bayyana cewa anyiwa jawabin nasa lauje a cikin nadi wato ba’a bayyana ta kamar yadda take ba.

Inda Buhari yayi karin haske kan maganar da ta janyo masa suka a shafukan sada zumunta musamman daga matasan kasar.

A kwanan nan nai dai Shugaban Najeriya ya ce matasa da dama basu yi makaranta ba, kuma suna son ababen more rayuwa kyauta.

Shugaba Buhari ya sake yin tsokaci akan matasan Najeriya
Shugaba Buhari ya sake yin tsokaci akan matasan Najeriya

Ya ce: "Toh ka san Najeriya an ce mun kai miliyan 180 ko kuma miliyan maitan.

"Kuma 60 bisa 100 na su duk matasa ne, wato shekara 30 abin da ya yi kasa, mu kamar a Arewa ba su yiu makaranta ba, koko suna yi sun fita.

"Toh, baya ga dai Allah Ya sa damunan bara da ta bana ta yi albarka, yawancin su ba su da aikin yi. Suna zaune.

"Irinsu ko sun je kamar misali kudu, abin da za su samu bai ma isa su biya kudin gidan haya ba, balle abin da za su ci su sha su yi sutura ko kuma su koma gida."

Ya ce miliyoyin matasa ne suka samu aikin yi ta hanyar noma, amma 'yan jarida ba su bayyana wannan ba.

KU KARANTA KUMA: Kalli hoton mace ta farko dake tuka jirgin sama daga jihar Katsina

Shugaba Buhari ya kara da cewa: "Su kuma dama 'yan jarida na Najeriya balle na rubutawa a.. kusan abin da suka ga dama suke yi.

"Yanzu kaman nasara da aka ci a noma da bara da bana, miliyoyin mutane sun je gona, sun yi aiki kuma abin ya yi albarka. Amma ka ga ba'a maganar. Miliyoyi! sai kullum a tashi ana zage-zage."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel