Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya bayar da umurnin daukan sabbin 'Yan sanda 6000

Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya bayar da umurnin daukan sabbin 'Yan sanda 6000

A kokarin sa na magance rikice-rikicen makiyaya da manoma da ke afkuwa a wasu sassan Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin daukan sabbin 'yan sanda 6000 saboda inganta tsaro.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne a watan hira na musamman da ya yi da gidan rediyon muryar Amurka sashin Hausa a ranar Talata a birnin Washington DC da ke kasar Amurka.

Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya bayar da umurnin daukan sabbin 'Yan sanda 6000
Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya bayar da umurnin daukan sabbin 'Yan sanda 6000

Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara Amurka ne sakamakon gayyata da shugaba Donald Trump na Amurka ya aike masa.

KU KARANTA: Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 9 da sukayi aure tsakaninsu

"Zamu kara daukan matakai don magance kallubalen tsaro a kasar ciki har da daukin sabbin Yan sanda da horas da su.

"Na bayar da umurin daukan sabbin Yan sanda 6000 wanda za'a dauka daga kananan hukumomi 776 da ke kasar.

"Ko da mutum daya za'a dauka daga kowane karamar hukuma, hakan za'ayi a maimakon zuwa tashohin mota, ko tashohin jiragen kasa ko kasuwanni don daukan sabbin yan sandan.

"Umurnin da na bawa hukumar Yan sandan kenan," inji Buhari.

A kan batun kafa Yan sandan jihohi da wasu gwamnonin jihohi ke yi, shugaba Buhari ya ce a halin yanzu dai kamata ya yi ayi biyaya ga kundin tsarin mulki da ya bawa gwamnatin tarayya ikon horas da Yan sandan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel