Yansanda sun sako Shehu Sani bayan ya amsa gayyatarsu game da zargin tafka laifin kisa

Yansanda sun sako Shehu Sani bayan ya amsa gayyatarsu game da zargin tafka laifin kisa

Sanatan mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ya amsa gayytar da rudunar Yansandan jihar ta yi masa dangane da zargin aikata laifin kisan kai da ake yi masa, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Sani ya bayyana haka ne ta shafinsa na Twitter, inda yace “Na amsa gayyatar da rundunar Yansanda ta yi min, inda na rubuta bayanin abinda na sani, sa’annan suka kyale ni na tafi saboda mukami na da mutunci na.

KU KARANTA: Jami’an hukumar Kwastam zasu samu karin albashi mai tsoka nan gaba kadan – Hamid Ali

“Yansandan sun bukaci na bayyana a gabansu da misalin karfe 10:45 na safiyar ranar Litinin, haka kuwa aka yi, inda na isa babban ofishin Yansandan jihar a daidai 10:45, na bada bayanina a iyakar gaskiyata, sa’annan suka bada beli na, na yi gaba.” Inji shi.

Yansanda sun sako Shehu Sani bayan ya amsa gayyatarsu game da zargin tafka laifin kisa
Shehu Sani

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a kwanakin baya ne dai Yansanda suka nemi Sanatan ya bayyana a gabansu don amsa tambayoyi da suka shafi zargin hannu cikin aikata laifin kisan kai, inda kwamishinan Yansandan jihar Austin Iwar ya mika gayyatar ta hannun Akawun majalisun dokokin Najeriya.

Wani matashi da aka kama da laifin kisan kai, Isah Garba ne ya kira sunan Shehu Sani da haidminsa Bashir Hamdada cikin maganan, inda yace yana da hannu cikin kashe wani matashi mai suna Lawal Madugu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng