Hukumar 'yan sanda ta dakume wani dan takarar gwamna a jihar Adamawa, ta bayar da dalili
- Hukumar 'yan sanda a jihar Adamawa ta kama dan takarar gwamna a jihar, Abel Behora, karkashin jam'iyyar SDP
- Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar, SP Othman Abubakar, ya tabbatar da kama Behora bisa kalaman tunzuri da karya da gan-gan
- Hukumar ta 'yan sanda ta ce zata gurfanar da shi a gaban kotu bisa caji guda hudu
Hukumar 'yan sanda a jihar Adamawa ta kama dan takarar gwamna a jihar karkashin jam'iyyar SDP, Abel Behora.
Kakakin hukumar 'yan a jihar Adamawa, SP Othman Abubakar, ya tabbatar da cewar sun kama Behora saboda wasu kalamai na tunzuri da yin karya da gan-gan domin tayar da fitina a wani shirin gidan Rediyo.
An kama Behora ne a jiya kuma hukumar 'yan sanda ta ce zata gurfanar da shi gaban kotu bisa wasu caji guda hudu da suka hada da bata suna da kuma bayar da bayanan bogi a kan hukumar 'yan sanda.
Abubakar ya bukaci 'yan siyasa da su yi harkokin su bisa doka da tsari tare da bayyana cewar hukumar 'yan sanda zata tabbatar da an samu zaman lafiya mai dorewa a jihar.
DUBA WANNAN: Kasar Saudiyya ta zartar hukuncin kisa kan matashin da ya yi ridda tare da yin batanci ga Annabi
A jiya Legit.ng ta wallafa wani labari dake nuna cewar wasu 'yan jam'iyyar APC a jihar Adamawa sun bayyana 'ya'yan jam'iyyar da basu halarci taron yakin neman zaben Buhari ba da cewar suna cin dunduniyar jam'iyyar.
Jaridar Guardian ta rawaito cewar gwamnan jihar Adamawa, Mohammed Jibrilla Bindow, da jami'an gwamnatin sa basu halarci wurin taron kaddamar da yakin neman zaben Buhari ba da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawan, zai jagoranta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng