Jami’an hukumar Kwastam zasu samu karin albashi mai tsoka nan gaba kadan – Hamid Ali
Shugaban hukumar yaki da fasa kauri, Kanal Hamid Ali mai murabus, ya kaddamar da wata kwamiti mai kunshe da mutane 9 da zasu duba karin albashi ga jami’an kwastam da alawus alawus, kamar yadda jaridar Ship and Ports Daily ta ruwaito.
Shugaban hukumar kwastam, Hamid Ali ya nada babban hadiminsa, Birgediya Janar Buhari I a matsayin shugaban kwamitin, inda ya baiwa mambobin kwamitin tabbacn rahotonsu zai yi amfani wajen inganta walwalar ma’aikatan hukumar.
KU KARANTA: Manyan jiragen ruwa guda 32 dauke da man fetir da kayan abinci na gab da isowa Najeriya
Majiyar Legit.ng ta ruwaito da ma can Hamid Ali ya sha amsa korafin da jami’an hukumar ke yi game da karancin albashinsu, da cewa zai yi musu karin albashi nan bada jimawa ba, a nan ma Ali yace zai tabbatar da karin albashin ma’aikatan Kwastam kafin karshen shekara.
Wata takarda da ta fito daga ofishin shugaban hukumar, kuma ta samu sa hannun mataimakin shugaban hukumatr, ACG Abdulkadir Azarema ta umarci kwamitin ta danganta albashin kwastam da na ma’aikatan hukumar tattara harajin gwamnatin tarayya.
An baiwa kwamitin sati biyu ya kammala aikinsa, inda aka umarce shi ya duba rahotannin da aka samu a baya na neman karin albashi, tare da fitar da rahoto guda daya daya cikinsu, don mika ma shugaban hukumar, tare da aika ma hukumar kayyade albasussuka kwafin rahoton.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng