Wata Jami’ar Mata a Sudan ta karrama Gwamna Geidam da Dakta

Wata Jami’ar Mata a Sudan ta karrama Gwamna Geidam da Dakta

- Wata Jami’a a da ke can Kasar Sudan ta karrama Gwamnan Jihar Yobe

- Jami’ar da ke Omudurman tace Gwamna Geidam yayi wa mata kokari

- Duk da rikicin Boko Haram dai Gwamnan yayi abin a zo a gani a Jihar

Wata Jami’ar Mata a da ke Garin Omdurman Kasar Sudan ta karrama Gwamnan Jihar Yobe Mai Girma Alhaji Ibrahim Geidam da Digirin Dakta saboda kokarin sa a wajen habaka harkar ilmi da inganta rayuwar mata duk da rikicin Kasar.

Wata Jami’ar Mata a Sudan ta karrama Gwamna Geidam da Dakta
Jami'ar Ahfad tace rikicin Boko Haram bai hana Geidam aiki ba

Mai magana da yawu bakin Gwamna Ibrahim Geidam watau Abdullah Bego ya bayyanawa Jaridar Daily Trust cewa Jami’ar Ahfad ta Mata da ke Kasar Sudan ta jinjinawa kokarin da Gwamnan yake yi wajen taimakawa mata masu ciki.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gana da Donald Trump a Amurka

Jami’ar ta Ahfad ta lura da katafaren asibitin koyon aikin da Gwamnan Yobe ya ke ginawa a Jihar na Jami’ar YSU. Haka zalila dai a Jihar Yobe kyauta ake duba masu juna biyu da kuma yara ‘yan kasa da shekaru 5 inji Kakakin Gwamnan.

Bayan wannan kuma dai Gwamnatin Geidam ta tura yara sama da 1400 zuwa Jami’o’in kasar waje domin yin karatun Digiri da Digirgir da sauran su. Daga cikin kasashen da aka tura ‘Daliban Jihar har da kasar Sudan da ta karrama Gwamnan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng