Manyan jiragen ruwa guda 32 dauke da man fetir da kayan abinci na gab da isowa Najeriya
- Manyan jiragen ruwa guda 23 sun nufo Najeriya dauke da kayan abinci
- Manyan jiragen ruwa guda 9 sun nufo Najeriya dauke da man fetir
Akalla jiragen dakon mai guda 32 suna gab da isowa Najeriya, ta jihar Legas, dauke da kayan abinci da man fetir, inda ake sa ran zasu fara sauke kaya tun daga ranar 30 ga wata Afrilu zuwa 8 ga watan Mayu.
Kamfanin dillancin labaru,NAN, ne ta ruwaito jiragen zasu fara sauke kayan ne a ranar Litinin, a tashoshin jiragen ruwa na Tincan Island da Apapa, inji sanarwar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa na Najeriya.
KU KARANTA: Yansandan Najeriya sun yi caraf da wani Dan daba da ya daɓa ma abokinsa wuƙa
Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin jiragen 32, guda 9 zasu shigo ne dauke da man fetir, yayin da sauran guda 23 suke dauke da kayayyakin abinci, da suka hada da alkama, kifi, man Disil, sundukai, taki, da sauran kayayyaki.
Sanarwar ta kara da cewa tuni jiragen ruwa guda 10 sun isa jihar Legas dauke da taki da man fetir don amfanin yan Najeriya, da kamfanoni.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng