Abinda zai warware matsalolin tsaron Najeriya fiye da amfani da karfin hukuma - Tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon
- Janar Yakubu Gowon ya bukaci shugabannin addinin Kirista da su dage da yiwa Najeriya addu'o'i
- Ya bayyana cewar addu'a ce hanya mafi sauki da sauri da zata magance kalubalen tsaro dake damun Najeriya
- Gwamna Rochas ya roki malaman addinin Kirista da su cigaba da wa'azin a zauna lafiya
Da yake jawabi jiya a cocin First Baptist dake Owerri ta jihar Imo, tsohon shugaban kas, Janar Yakubu Gowon, ya bukaci shugabannin addinin Kirista da su cigaba da yiwa Najeriya addu'o'in samun zaman lafiya.
Gowon ya ce addu'o'in shugabannin addinin Kirista ba zasu fadi kasa a banza ba tare da bayyana masu cewar addu'a ce kadai hanyar da zata iya magance matsalolin kasar nan cikin sauki da sauri.
Tsohon shugaban kasar ya ce babu shakka ubangiji zai amsa addu'o'in 'yan Najeriya kuma zai yi maganin duk wani ciwo dake damun ta.
Da yake waiwaye adon tafiya, Gowon, ya ce lokacin da ta tabbata cewar zai shugabanci Najeriya a mulkin soji, abu na farko da ya fara yi shine neman taimakon ubangiji bayan yi masa godiyar bashi damar mulkin Najeriya da ya yi.
DUBA WANNAN: Zargin yunkurin kashe gwamna: Ana nuna yatsa tsakanin APC da PDP
A jawabin sa, gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya roki malaman addinin Kirista da su cigaba da yin wa'azin zama lafiya.
Okorocha ya bukaci kiristoci da kada su bari kashe wasu 'yan uwan su a wasu wuraren ya harzuka su ya zuwa daukar fansa tare da yi masu tunin cewa Yesu Almasihu bai yarda da daukan fansa ba saidai yafiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng