Kasar China za ta taimakawa Najeriya wajen samar da isassun gidaje
- Gwamnatin Buhari na kokarin samar da isassun gidaje a Najeriya
- Kasashe irin su China za su taimaka wajen ganin an ci ma hakan
- Wani kamfani a Kasar yayi alkawarin sa kudin sa a aikin da za ayi
Kasar Sin watau China ta nuna cewa a shirye ta ke da ta narka kudin ta wajen gine-ginen gidajen da za ayi a Najeriya domin ganin an rage matsalar da ake fama da shi na karancin gidajen zama.
Mun samu labari daga Jaridar All Africa a karshen makon can cewa Kamfanin One Belt One Road da ke Kasar ta China za ta shiga cikin aikin gina gidaje a Kasar da za ayi. Shugaban wannan Kamfani Jin Changsheng yayi alkawarin hakan.
Mista Jin Changsheng ya bayyana wannan ne a wani taro da aka shirya kwanaki a Abuja. Mutanen kasar ta Chona sun fi shekaru 30 su na harkar gine-gine don haka sun kware kuma za su taimakawa wajen rage karancin gidajen da ake fama da su.
KU KARANTA: PDP ta fadawa Shugaban kasa Buhari ya daina yaudarar kan sa
An shirya taron domin kokarin jawo hankalin ‘Yan kasuwa da magina zuwa Najeriya inda ake kokarin gina gidaje 3000 a Birnin Tarayyan Abuja. Gwamnatin Tarayya na kokarin samawa kananan Ma’aikata da ‘yan tsaka-tsakiya gidaje ne a Najeriya.
Kwanakin Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari za ta gina gidaje na sama da Naira Biliyan 1.3 a Jihar Sokoto.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng