Nifa ban ce a tsige shugaba Buhari ba - Sanata Urhoghide

Nifa ban ce a tsige shugaba Buhari ba - Sanata Urhoghide

- Sanata Urhoghide yace musanta labaran da ke yawa a kafafen yadda labarai inda ake cewa ya bukaci a tsige shugaba Buhari

- Sanatan yace kawai ya ce zai tabbatar da cewa shugaba Buhari yayi wa majalisa bayyani dalilin da yasa fitar da kudi ba tare da sanar da majalisa ba

- Sanatan yace tsigewa ba karamin abu bane kuma shi ba abinda yake nufi ba kenan

Sanata Mathew Urhoghide mai wakilitan mazabar kudancin Edo ya musanta cewa ya gabatar da bukatar tsige shugaba Muhammadu Buhari.

Dan majalisar wanda ya gabatar da kudirin tatance hallascin fitar da kudi daga asusun rarar man fetur da shugaba Buhari yayi don siyan jiragen saman yaki daga kasar Amurka yace mutane sun canja abinda ya fadi ne.

Sanata ya ce ya tuba, kuma shi bai ce a tsige Buhari ba
Sanata ya ce ya tuba, kuma shi bai ce a tsige Buhari ba

Urhoghide yace shi bai taba cewa a tsige shugaba Buhari ba, kawai dai ya janyo hankalin Majalisar ne zuwa ga sashin kundin tsarin mulki da yayi magana kan ka'idojin fitar da irin wannan kudin saboda shugaban kasa yayi musu bayanin dalilin da yasa ya fitar da kudin siyan jiragen guda 12.

KU KARANTA: Wani babban Fasto ya shawarci Kiristoci su dena aibanta shugaba Buhari

Kalamansa: "Shugaban kasa ya siyo jiragen yakin ne da kyakyawan nufi amma akwai kuskure cikin hanyar da ya bi. Shima kansa ya amsa cewa ya yi kuskure. Mu ('Yan majalisa) munyi rantsuwa cewa zamu kare kundin tsarin mulkin kasa.

"Tsige shugaban kasa abu ne mai tsawo kamar yadda zaka gani idan ka duba sashi na 143. Da farko dole sai anyi bincike kuma a gabatar da sakamakon binciken a rubuce, sannan kuma shugaban Majalisa ya rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa.

"Shima shugaban kasa zai amsa wasikar kuma hakan zai dauki lokaci mai tsawo. Bamu kai ga zancen tsige kowa ba. Babu wanda yayi maganar tsige shugaban kasa a gaban Majalisa."

Ya kara da ce idan dai kafafen yadda labari sun bayar da rahoto cewa wani yace a tsige shiugaban kasa, sunyi hakan ne cikin kuskure.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164