Wata kasar Afirka ta halasta amfani ta ganyen wiwi

Wata kasar Afirka ta halasta amfani ta ganyen wiwi

- Gwamnatin kasar Zimbabwe ta hallasta amfani da ganyen wiwi don yin magani da binciken kimiyya

- A sabuwar dokan, duk wanda yake son fara noman wiwi din sai ya nemi izini a rubuce daga ma'aikatan lafiya na kasar

- Gwamnatin kuma zata rika sanya idanu kan wanda suka karba lasisi don ganin cewa sunyi amfani dashi kamar yadda dokar ta tanada

A wata sabuwar doka, kasar Zimbabwe ta hallasta noman ganyen wiwi domin amfani dashi wajen yin magunguna da binciken kimiyya kamar yadda jaridar AFP Saturday ta ruwaito.

Dokar tace mutane suna iya neman lasisi daga ma'aikatan lafiya don fara noman ganyen wiwi din amma kawai za'a rika amfani dashi ne saboda magani da kuma binciken kimiyya kuma hukuma zata sanya ido akan manoman.

Wata kasar Afirka ta halasta amfani ta ganyen wiwi
Wata kasar Afirka ta halasta amfani ta ganyen wiwi

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Sojin Saman Najeriya sunyi ragaraga da sansanin yan Boko Haram da ke Tumbum Gini

Dokar kuma tace dole duk wanda zai nemi izinin fara noman sai ya kasance dan kasa ne kuma idan kamfani ce ta son noman itama sai ta gabatar da takardan shaidan kafa kamfanin kuma gwamnati zata rika sanya ido akansu.

A baya, laifi ne amgani da ganyen wiwi a kasar Zimbabwe duk da cewa wasu mutane musamman masu maganin gargajiya suna amfani dashi wajen maganin farfadiya, asthma, hauka inda wasu kuma kawai suna amfani dashi ne don nishadi ko gyaran gashin kai.

Duk da haka duk wanda aka samu dauke da ganyen wiwi din mai yawa yana iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 12 a gidan kurkuku idan ba mai rajista da hukuma bane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel