An samu dai-daito a garin Akure bayan rikicin da aka samu tsakanin Hausawa da Yarabawa

An samu dai-daito a garin Akure bayan rikicin da aka samu tsakanin Hausawa da Yarabawa

- An samu dai-dai to a garin Akure, babban birnin jihar Ondo, bayan rikicin daya gabata tsakanin Hausawa da Yarabawa mazauna yankin Sabo-Odojoka bayan da gwamnatin jihar da kuma wasu manya masu fada aji a jihar irin su Deji na Akure, Oba Ogunlade Aladelusi II suka shiga tsakanin kabilun domin sulhu. Manyan mutanen da kuma wakilan gwamnatin jihar sunyi Allah wadai da rikicin, sannan sun kai ziyara wurin da lamarin ya faru tun ma kafin rikicin ya lafa a ranar Litinin

An samu dai-daito a garin Akure bayan rikicin da aka samu tsakanin Hausawa da Yarabawa
An samu dai-daito a garin Akure bayan rikicin da aka samu tsakanin Hausawa da Yarabawa

An samu dai-dai to a garin Akure, babban birnin jihar Ondo, bayan rikicin daya gabata tsakanin Hausawa da Yarabawa mazauna yankin Sabo-Odojoka bayan da gwamnatin jihar da kuma wasu manya masu fada aji a jihar irin su Deji na Akure, Oba Ogunlade Aladelusi II suka shiga tsakanin kabilun domin sulhu. Manyan mutanen da kuma wakilan gwamnatin jihar sunyi Allah wadai da rikicin, sannan sun kai ziyara wurin da lamarin ya faru tun ma kafin rikicin ya lafa a ranar Litinin.

DUBA WANNAN: Duniya tazo karshe: Za'a hana kiran Sallah a kasar Norway

Gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Rotimi Akuredolu, wanda mataimakin sa Mista Agboola Ajayi ya wakilce shi, yayi kira ga al'ummar Hausa dasu yi hakuri a zauna lafiya. Deji na Akure, tare da wasu manyan masu fada aji a jihar, sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda suka nemi da jama'a suyi hakuri su kwantar da hankalin su. Sannan kuma ya gargadi mutanen sa da kada su takura wa al'ummar Hausawan yankin, sannan kuma ya gargadi Hausawan akan kada su takura wa Yarabawan yankin.

Sarkin, wanda yace duka Hausawa da Yarabawa al'umma daya ce bai ga abin tada rikici a tsakanin su ba, sannan yayi alkawarin hada taro na dukkanin kungiyoyin da abin ya shafa tare da gwamnan jihar domin tabbatar da zaman lafiya a babban birnin jihar. Majiyarmu Legit.ng ta gano cewar, gwamnatin jihar ta shirya taron jim kadan bayan an gayyaci dukkanin mutanen da abin ya shafa.

Elijoka, Cif Taiwo Afolabi, wanda yake shine shugaban gargajiya na yankin Sabo-Odojoka, ya ce anyi kwanaki da dama, ana sanarwa a garin Akure cewar za ayi bikin gargajiya na Egungun, saboda haka duk wanda ba zai halarta ba ya zauna a gida, domin kuwa za'a rufe tituna da dama a yankin.

Cif Afolabi, wanda aka sakawa motar shi wuta tare da wasu motoci guda hudu, yace bikin na kwana daya ne kawai, kuma kowa a yankin yasan duk shekara muna gabatar da bikin.

Anyi kokarin yin magana da Hausawa mazauna wurin, inda suka tabbatar da cewar komai ya dawo dai-dai

An bayyana sunan matar da ta rasa ranta a dalilin fitowa da tayi domin neman danta da suna Mama Lekan, wacce ta fadi a lokacin da ake rikicin a take tace ga garin ku nan.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Femi Joseph, ya shaidawa manema labarai cewar suna gabatar da kwakkwaran bincike akan lamarin, amma har yanzu ba a kai ga samun gaskiyar mine ya faru ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: