Biri yayi kama da mutum: An kama dan Boko Haram cikin masu kai hare-hare a jihar Binuwai
Hukumar Sojin Najeriya ta bayar da sanarwan kama wani gagarumin dan Boko Haram da ake kyautata zaton yana daya daga cikin masu kitsa hare-haren da ake kaiwa a wasu sassan jihar Benuwe.
Sanawarn tace an kama Aminu Yaminu ne wanda akafi sani da Tashaku a yau Juma'a a garin Makurdi, babban birnin jihar Benue yayin da wasu ayarin hadin gwiwa wanda suka hada da jami'an tsaro na musamman na 707, Jami'an Yan sanda da 'Yan sandan farin kaya DSS.
Bayan an kama shi, an gano cewa Aminu ya kammala shirye-shiryen kai wasu miyagun hare-haren a wasu garuruwan Benuwe tare da taimakon abokansa daga jihohin Bauchi, Borno, Yobe da Nasarawa kamar yadda sanarwar da ta fito daga bakin mai magana da yawun 707 Special Forces Brigade, Olabisi Olalekan Ayeni ta bayyana.
KU KARANTA: Akwai masu daukan nauyin makiyaya masu kai hari a Binuwai - Sojin Najeriya
Ayeni yace kama Aminu yana daya daga cikin ayyukan da hukumar Sojin keyi don ganin an dawo da zaman lafiya a Jihar Benuwe tare da kama dukkan batagarin da suka adabi jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng