'Yan sanda sun damke masu garkuwa da mutane, sun kuma ceto jariri dan wata 17 da aka sace
- Wasu mutane hudu sunyi garkuwa da jariri dan watanni 17
- Iyayen yaron sun biya kudi N627,000 domin a sakar musu dansu
- Hukumar yan sanda ta Imo ta cafke mutane biyu daga cikinsu
Jami'an hukumar Yan sanda masu yaki da fashi da makami (FSARS) ta jihar Imo sun cafke wasu mutane biyu daga cikin wadanda sukayi garkuwa da jariri dan watanni 17.
DUBA WANNAN: Da watakila ina cikin makiyaya ana fafatawa dani - Shugaba Buhari
Mai magana da yawun hukumar, ASP Lfy Ezeudeogu yace wasu mutane hudu ne sukayi garkuwa da jaririn a ranar Asabar.
Ezeudeogu, wanda wa mikawa mahaifiyar jaririn danta bayan ceto shi da sukayi yace wadanda ake zargin sun shiga gidan masu iyayen jaririn ne sukayi musu fashi sannan sukayi sace jaririnsu.
Ta kuma ce wadanda ake zargin sun kwace katin cirar kudi ATM na mahaifiyar yaron.
Tace wadanda ake zargin sun nemi kudi N627,000 amma sunki su bada yaron bayan sun karbi kudin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng