Gayyatar Shugaba Buhari zuwa Fadar White House alama ce ta kyakkyawar dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka - Lai Muhammad

Gayyatar Shugaba Buhari zuwa Fadar White House alama ce ta kyakkyawar dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka - Lai Muhammad

Ministan Labarai da al'adu na Najeriya Alhaji Lai Muhammad, ya bayyana cewa gayyatar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari alama ce dake nuna kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin ganawa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na Najeriya a birnin New York na kasar Amurka, inda ya bayyana nasarorin da gwamnatin shugaba Buhari ta samarwa kasar Amurka da duniya baki daya.

Gayyatar Shugaba Buhari zuwa Fadar White House alama ce ta kyakkyawar dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka - Lai Muhammad
Gayyatar Shugaba Buhari zuwa Fadar White House alama ce ta kyakkyawar dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka - Lai Muhammad

Legit.ng ta fahimci cewa, ana sa ran shugaba Buhari zai ziyarci fadar White House ta shugaba Donald Trump a ranar Litinin 30 ga watan Afrilu, inda zasu tattauna kan batutuwan yaki da ta'addanci da kuma tattalin arziki.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Najeriya ta zargi Sheikh El-Zakzaky da laifin Kisan Kai

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya kuma ruwaito cewa, shugaba Buhari zai kasance shugaban nahiyyar Afirka na farko da za a yi maraba da shi a fadar White House tun hawa karagar mulki ta Trump a ranar 20 ga watan Janairun 2017.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, shugaban na Najeriya shine shugaba na farko a nahiyyar ta Afirka da shugaba Trump ya gana da shi ta hanyar wayar salula bayan an rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Amurka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng