Idan ajali ya yi kira sai an je: wata yar bautar kasa ta mutu a sansanin horas da yan bautan kasa

Idan ajali ya yi kira sai an je: wata yar bautar kasa ta mutu a sansanin horas da yan bautan kasa

Waya yar bautan kasa mai suna Eva Iche Amadi ta gamu da ajalinta a sansanin horas da yan bautan kasa na jihar Kwara, dake garin Yikpata, cikin karamar hukumar Edu na jihar, inji rahoton jaridar Sahara Reporters.

Yar bautan kasar, wanda ta kammala karatu a jami’ar ilimin kimiyyar mai da iskar gas dake garin Fatakwal na jihar Krosribas, inda ta samu karaya sakamakon wani atisaye da suka yi a ranar 23 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Sanata Kabiru Marafa ya fallasa sunayen mutane 21 da ya samar ma aiki da sunayen ma’aikatun

Faruwar hakan ke da wuya sai aka garzaya da ita dakin shan magani dake cikin sansanin, sai dai wasu majiyoyi na karkashin kasa sun tabbatar da cewar Eva ta mutu ne sakamakon rashin isashshen kayan aiki a sansanin.

Idan ajali ya yi kira sai an je: wata yar bautar kasa ta mutu a sansanin horas da yan bautan kasa
Marigayiya

“Ta samu karaya ne a yayin da muke atisayen Man or War, inda muka garzaya da ita dakin shan magani, amma muka tarar babu na’urar daukan hoto, babu magani, babu komai, don hatta bandeji ma siya ta yi da kudinta.” Inji majiyar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito nisan asibitin dake kusa da sansanin ya kai tafiyar awanni biyu, wanda hakan ya taimaka wajen ta’azzar ciwon da yan bautan kasar ke fama da shi, wanda yayi sanadin mutuwarta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: