A Maraya na tashi wajen Mahaifiya ta kuma na san maganin talaucin Najeriya – Atiku

A Maraya na tashi wajen Mahaifiya ta kuma na san maganin talaucin Najeriya – Atiku

- Atiku ya bayyana hanyar da za a magance talauci a kasar nan

- Tsohon Mataimakin Shugaban kasar yace zai karfafawa mata

- ‘Dan kasuwan yace mata ne za su fitar da mutane daga kangi

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya dage wajen yunkurin sa na neman shugabancin kasar nan inda ya je ‘Dakin taro da tarihi na Chatham house da ke Landan kwanan nan yayi wani jawabi.

A Maraya na tashi wajen Mahaifiya ta kuma na san maganin talaucin Najeriya – Atiku
Babban ‘Dan kasuwan Atiku Abubakar yace da mata zai yi amfani

Babban ‘Dan siyasar na Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya tashi ne yana Maraya kuma Mahaifiyar sa ce ta rike sa har ya kai inda ya kai. Atiku ta kai ya bude ‘dan karamin bankin gari wanda ya samawa jama’a aikin yi.

KU KARANTA: Atiku Abubakar yayi jawabi a Chatham house

Babban ‘Dan kasuwar yake cewa a lokacin da ya kafa wannan karamin banki, kusan akasarin wadanda aka rika ba bashi domin su samu jarin kasuwanci mata ne. Atiku yace a sanadiyyar haka sama da iyalai 45, 000 su ka amfana a kasar.

Wazirin na Adamawa ya nuna cewa kusan duk wanda aka ba bashin nan sai da su ka maido kudin aron don haka yace in ka na neman abin da zai kawo karshen talauci a Yankin nan ka karfafawa mata da kasuwanci sai al’umma ta fita daga kangi.

A baya Legit.ng ta rahoto maku cewa Tsohon Mataimakin Shugaban kasar Atiku Abubakar yace da zarar ka ba namiji jari babu abin da zai yi sai dai ya karo aure ya tara iyali kurum.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng