Sanata Kabiru Marafa ya fallasa sunayen mutane 21 da ya samar ma aiki da sunayen ma’aikatun
Duk lalacewar yanayi, da zafinsa, tabbas akwai wadanda zai yi ma dadi, sai dai yawancin wadanda zasu amfana sai sun kasance masu uwa a gindin murhu, kwatankwacin haka ne ya faru a jihar Zamfara, inda wani Sanata ya bayyana sunayen mutanen da ya samar ma aikin yi.
Legit.ng ta ruwaito wakilin al’ummar Zamfara ta tsakiya a majalisar Dattawa, Sanata Kabiru Marafa ya bayyana sunayen mutane ashiri da daya, 21, a shafinsa na Facebook, wadanda ya samar ma aikin yi a manyan ma’aikataun gwamnati.
KU KARANTA: Babban sufetan Yansandan Najeriya ya yi watsi da umarnin majalisar Dattawan Najeriya
Ya bayyana jerin sunayen nasu kamar haka:
1-Fatima abubakar - NNPC
2-Kabiru sani Gusau - NIMC
3-Isah labaran - FRSC
4-Aina-u jabar - CBN
5-Farida labaran - CBN
6- Faisal sani - FRSC
7- Zayyanu bala - RAILWAY
8- Bello aliyu - SARS
9- Anas Atiku - SARS
10- Fodio sani - INTERIOR
11- Jamila habibu - INTERIOR
12- karima habibu - NNPC
13- Nana sani - NATIONAL ASSEMBLY
14- Fiddausi shehu - NATIONAL ASSSEMBLY
15- Yakubu Ahmad - NECO
16- Faruk musa - NECO
17- Abdullahi mustapha - NECO
18 - Amina na gwaggo - NECO
19- Fatima yusuf - NNPC
20- Ibrahim alkarama - NNPC
21- umar sani Gusau - NIMC
Daga karshe Sanatan ya umarce duk wanda sunansa ya fado cikin wadanda suka rabauta su garzaya ofishinsa a ranar Juma’a, 27 ga watan Afrilu don amsar takardunsu na fara aiki.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng