Rikicin Benuwe na neman daukan sabon salo, an kone masallatai

Rikicin Benuwe na neman daukan sabon salo, an kone masallatai

A kalla mutane 25 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon barkewar rikice-rikice a cikin kwanakin nan a wasu garuruwa dake jihar Benue.

Har ila yau, mutane da dama sun jikkata kuma an anyi asarar dukiyoyi wanda aka kone su sakamakon hare-haren da ke kama da na ramuwar gayya wadanda ake zargin yan kabilar Tivi da kaiwa Musulmi wanda galibinsu Hausawa ne.

An kona masallatai biyu a jihar Benuwai
An kona masallatai biyu a jihar Benuwai

Kamar yadda muka samo daga kafar yadda labarai na BBC, babban limamin masallacin izala na Makurdi, Sheikh Shuaibu, yace an kona masallatai guda biyu wadanda ba'a dade da gyara su ba sakamakon kona su da akayi a wata rikicin a baya.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun gano miyagun makamai masu dimbin yawa a wata jihar Arewa

Sheikh Shuaibu ya cigaba da cewa ya ga gawawakin Musulmi da aka kashe guda 27 a yayin da ya ziyarci asibitin koyarwa da ke birnin Makurdi, ya kuma ce akwai mutane da dama da ake nema amma ba'a gansu ba.

Limamin yace a halin yanzu an fara samun zaman lafiya a garin duk da cewa rikicin yafi zafi ne a garuruwan da ke wajen gari.

A bangarensa, shugaban kabilar Tivi, Tar Makurdi Cif Sule Abenga, ya bayyana cewa akwai alamun rikicin zata iya kamari tun bayan harin da aka kai wani coci inda aka kashe limamai biyu tare da mabiyansu.

Basaraken yace sunyi iya kokarinsu na ganin cewa rikicin ta tsaya iya nan amma basu san cewa akwai wadanda suka dauki abin da zafi har kuma zasu iya aikata ta'asa haka ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164