Yunkurin majalisar dattijai na tsige Buhari ya gamu da cikas

Yunkurin majalisar dattijai na tsige Buhari ya gamu da cikas

- Majalisar dattijai na kokarin tsige shugaba shugaba Buhari daga mulki a kan batun sayen jiragen yaki

- Shugaba Buhari ya fitar da Dalar Amurka $496 domin sayen jiragen yaki daga kasar Amurka

- Fitar da kudin ya fusata 'yan majalisar saboda Buhari bai tuntube su ba kafin zartar da hukunci

A yau, Alhamis, majalisar dattijai ta gaza yin amfani da sashe 143 na kundin tsarin mulki da ya bawa majalisa damar tsige shugaban kasa.

Majalisar dattijai na yunkurin tsige shugaba Buhari ne saboda ya sabawa sashe na 80 na kundin tsarin mulkin Najeriya wajen fitar da Dalar Amurka $496 daga asusun rarar man fetur domin sayen wasu jiragen yaki na musamman daga kasar Amurka ba tare da tuntubar majalisa ba.

Yunkurin majalisar dattijai na tsige Buhari ya gamu da cikas
Yunkurin majalisar dattijai na tsige Buhari ya gamu da cikas

Sanata Matthew Urhoghide ne ya fara gabatar da kudirin tsige Buhari sannan ya samu goyon bayan Sanata Chukwuka Utazi.

DUBA WANNAN: Rusau: Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta saka wa Ofishin yakin neman zaben Buhari jan fenti

Yanzu dai majalisar ta tura kudirin zuwa kwamitin ta na shari'a domin bayar da shawara. Ana saka ran kwamitin zai sanar da majalisar sakamako ranar Laraba mai zuwa.

Rahotanni sun bayyana cewar shugaban mmajalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, da Sanata Bala Ibn Na'allah ne suka dakile tattaunawa a kan kudirin tsigewar bayan Sanata Urhoghide da Utazi sun bijiro da ita.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng