Dubi yawan masu mika wa gwamnatin Najeriya bayanan sirri kan kudaden sata da aka boye, a bana kawai

Dubi yawan masu mika wa gwamnatin Najeriya bayanan sirri kan kudaden sata da aka boye, a bana kawai

- Kashi biyar bisa dari ga duk wanda ya tona kudaden sata ga gwanatin tarayya

- Wannnan ya sanya wasu sun zama biloniyas a dare daya

- Wasu da yawa sun kasa samun kudaden nasu saboda har yanzu batun yana kotu

Dubi yawan masu mika wa gwamnatin Najeriya bayanan sirri kan kudaden sata da aka boye, a bana kawai
Dubi yawan masu mika wa gwamnatin Najeriya bayanan sirri kan kudaden sata da aka boye, a bana kawai

Tun bayan da gwamnatin APC ta hau mulki ake kara samun labarin an kama makudan kudade da ake rasa masu su, wasu lokutan a gidaje, wasu lokutan a banki, kai har a gonaki ana gani. Wasu kuwa tsoro yasa suke dawo da kudaden.

Sai gwamnnati ta sanya lada ga duk wanda yasan inda aka binne kudaden Najeriya da aka sata, wadanta a yanzu an gano kusan tiriliyan daya, da 'yan siyasa suka kwashe suka mayar nasu da iyalansu, wasu har a kasar waje.

Ya zuwa yanzu dai, akalla mutum 8,000 ne suke sa rai zasu sami romon wannan lada da ake kira whistle blower policy, watau tonon-silili. Ka gano, ka tona, a baka kaso mai tsoka daga ciki.

DUBA WANNAN: Rigimar Larai da Turai: Iran ta mayar wa da Saudiyya martani

Executive Secretary na PACAC, Prof. Bolaji Owasonoye, ya gaya wa News Agency of Nigeria (NAN) a New York cewa, shirin ya sami karbuwa sosai da sosai.Sai dai yace, ba kowa ne ake baiwa kashi biyar dinba, inda yace idan kudaden sun kai biliyoyi, akan dai gutsurawa mutum ne amma ba za'a bashi wannan kaso ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel